Rahotannin daga gidan Rediyo na VOA Hausa na nuna cewa kiungiyar Boko haram ta bude gidan Rediyo wanda take amfani dashi wajen yada manufar ta da kuma musanta nasarorin da kasashen hadin gwaiwa suke samu akan ta.
Labarin wanda jaridar Dailytrust ta dauko ya nuna cewa wasu garuruwa dake kudancin Kasar Kamaru sun bayyana cewa suna kama tashar kuma suna sauraron abubuwan da take yadawa. Tashar ana kamata ne a karamin zango na 96.8 a garuruwan dake kusa da tashar.
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun farma garin Bita
Gwamnatin kasar kamaru inda aka tuntube ta ta bayyana rashin jin dadin ta akan aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa zata gudanar da bincike kuma ta kawo karshen gidan Rediyon. Gwamnatin ta bayyana cewa tana zargin cewa tashar tana a tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru din inda a nan ne suke yada manufofin su.
A Najeriya dai, sojojin Najeriya na cigaba da samun nasarori akan kungiyar Boko Haram inda aka cigaba da kashe mambobin ana kama wasu daga cikin su. Wannan ya sanya aka dakushe karfin kai hare-hare na kungiyar da abubuwan da take aikwatar a tarayyar Najeriya.
A wani labarin kuma, a makon daya wuce a kasar Nijar, yan kungiyar Boko Haram sun kai hari inda suka hallaka mutane da yawa sannan kuma suna yi sanadiyyar rasa dukiya mai dimbin yawa. Wannan ya auku ne a wani kauye dake kusa da iyakar N ajeriya da kasar ta Nijar.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHCElWtqb2tdl7ysu4yhmKuZnWLBonnBrpueZZeesaK6jKucnaGppHq3u8Bmn5qto5Z7qcDMpQ%3D%3D